Jiya Talata Power ta gana tare ‘yan gudun hijira a Sudan wadanda suka tsere daga Tigray, kuma ta sake jaddada matsayin Amurka, Majalisar Dinkin Duniya da sauransu cewa, abin da ake gani zai taimaki mutanan yankin Arewacin Habasha shine kawo karshen yakin da aka shafe sama da watannin tara ana yi.
Power ta fada a wani sakon twitter da ta wallafa jiya Talata cewa “Amurka tana kara matsa lamba ga dukkan bangarori a Tigray don su amince da tsagaita wuta nan take da fatan cewa mutane kamar ‘yan Habasha da na hadu da su a nan za su samu dama su koma gida.”
Rikicin ya kawo munanan hare-hare kan fararan hula, wanda ya shafin miliyoyi kuma dole ne a kawo karshen sa.
Ta ce musamman Amurka na yin kira ga kungiyar ‘Yan tawayen Tigray ko TPLF, da ta janye daga makwabtan ta na yankunan Amhara da Afar, domin gwamnatin yankin Amhara ta janye sojojinta daga yammacin Tigray, sannan makwabciyarta Eritrea ta gaggauta janye sojojin ta daga Habasha.