Yayinda yake hira da ‘yan jarida, babban sakataren kungiyar Dr. Justice Yankson ya ce wuraren da aka kafa domin kula da wadanda suka kamu da cutar sun fara cika da jama’a da suka kamu da cutar.
Yace asibitin koyarwa na Korle Bu da wasu manyan asibitocin kasar basu da wurare da zasu ajiye mutane da gwaji ya tabbatar da sun kamu da cutar.
Tuni sama da mutane 40 suka rasa rayukansu ta wannan annobar tsakanin watanni da cutar ta sake bulla a cikin kasar.
Shiko babban likita mai baiwa shugaban kasa shawara a kan harkokin kiwon lafiya Dr Anthony Nsiah Asare yace maida hankali kan matakan kariya shine abu mafi muhimmanci.
Da yake jawabi a karshen mako a kan halin da kasa ke ciki game da sake bullar cutar, shugaban kasa Nana Addo Dankwa Akufo Addo shima ya jaddada batun bin dokokin kariya da kuma batun rigakafi, inda yace gwamnati na nan kan bakanta na yiwa ‘yan Ghana miliyan 20 rigakafi karshen shekara, ya kuma kara da cewa gwamnati na duban yiwuwar samar da rigakafi na cikin gida, saboda karancin rigakafi a duniya na nufin mu fara yin na mu na gida kana mu rage dogaro da rigakafi daga kasashen waje don ya kamata mu wadatar da kan mu ta wannan fanni a nan gaba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: