A Jamhuriyar Nijar ‘yan bindiga sun hallaka mutum sama da 10 a yammacin ranar Lahadi a gundumar Bani-Bangou ta jihar Tilabery lamarin da ake kallonsa matsayin wani salon hanawa manoma gudanar da aiki a wannan lokaci na saukar damana.
A Jamhuriyar Nijar hukumomin kasar sun fitar da sakamakon jarabawar da suka shirya a watan Nuwamban 2020 domin tantance malaman da suka cacancin aikin karantarwa a makarantun sakandare a ci gaba da daukan matakan farfado da sha’anin ilimi.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun karbi wani ruunin tallafin allurar riga kafin covid 19 samfarin Johnson & Johnson a matsayin wata gudunmowa daga gwamnatin Amurka a karkashin shirin Covax mai amar da riga kafin wannan anoba ga kasashe masu karamin karfi.
Wani mai Shari’a babbar kotun Pietermaritzburg a lardin mahaifar tsohon shugaba na KwaZulu-Natal, ya dage sauararan karar tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma zuwa 10 ga watan Agusta.
A Najeriya yadda matsalar rashin tsaro ke kara yawaita na ci gaba da sauya tunanin ‘yan kasar har wasu na ganin hakan kan iya tarwatsa kasar.
An kama wani mai fada a ji na kungiyar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho a Cotonou da ke Jamhuriyar Benin.
Ma’aikatar ayyukan hajji ta ba dukan mata izinin gudanar da ayyukan haji ta tare da Mehrem ba, idan zasu tafi cikin gungun ‘yan’uwansu mata.
An yi hawan idin babbar sallah a yau Talata a dukkan fadin kasar Jamhuriyar Nijar inda shugaban kasar Bazoum Mohamed da sauran mukarraban gwamnati da suka raka shi wurin wannan hawan idin babbar sallar a babban massalacin Kaddafi na babban Birnin Yamai.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika gaisuwar bikin Eid El-Adha wanda ke gudana a duk fadin duniya.
Wani jami'i a fadar shugaban kasar Mali ya fada a ranar Talata cewa shugaban rikon kwarya Assimi Goita yana cikin "koshin lafiya" bayan da wasu mutane dauke da makamai suka far masa a lokacin bikin Sallah a Bamako babban birnin kasar.
Domin Kari