Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Boko Haram Ya Kashe Sojoji Biyar Da Wani Farar Hula a Kamaru


Wani yanki da 'yan bendiga suka kai hari a Najeriya
Wani yanki da 'yan bendiga suka kai hari a Najeriya

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe sojojin Kamaru biyar da wani farar hula a wani hari da suka kai a yankin arewa mai nisa na kasar, in ji ma’aikatar tsaron ranar Talata.

An kai harin ne a daren Litinin a kusa da kan iyaka da Najeriya, inda ayyukan kungiyar ke ci gaba da karuwa.

Sojoji uku da wani farar hula daya kuma sun jikkata a harin, a cewar sanarwar da aka karanta na gidan rediyon kasar.

Sanarwar ta ce, "wasu gungun 'yan ta'adda masu dauke da muggan makamai na kungiyar ta Boko Haram, a cikin wasu motocin yaki, sun kai hari kan kwamandan ... kusa da Zigue,"' yan kilomitoci kadan daga kan iyaka da Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, an kuma kashe wasu ‘yan ta’addan ba tare da yin karin bayani ba.

"Dakarun na ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana a duk yankin arewa mai nisa da kuma kan iyaka don hana ci gaba da kai hari," in ji ta. Kungiyar ta kara da cewa "ta dawo da karfi bayan sake fasalin cikin gida,".

Mambobin kungiyar Boko Haram da wata kungiyar da ta balle ta (ISWAP), na ci gaba da kai munanan hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula a yankin arewa mai nisa na Kamaru, da ma makwabtan Najeriya, Nijar da Chadi.

Suna yawaita sace fararen hula, musamman mata da yara.

XS
SM
MD
LG