Wannan ya biyo bayan harin ta’addancin da ya rutsa da su ne a ranar asabar din da ta gabata a kauyen Boni na gundumar Torodi dake jihar Tilabery iyakar Nijer da Burkina Faso.
Cikin salo irin na kwanton bauna ne ‘yan ta’adda suka yi nasarar hallaka jami’an tsaro a karshen mako inda motar dake dauke da rukunin farko na sojoji ta fada tarkon ‘yan bindigar akan hanyarsu ta kai kayan aiki wa wasu takwarorinsu dake tashar binciken a kauyen Bonin a gundumar Torodi da ke iyakar Nijer da Burkina Faso.
Sanarwar ma’aikatar tsaron kasar ta Nijer ta ci gaba da cewa motar ta 2 dake dauke da jami’an tsaro ta taka nakiya a lokacin da suke kokarin kai dauki a wadancan na farko. Abinda a jimilce ya yi sanadin mutuwar dakaru 15 sannan 6 sun yi batan dabo sai wasu 7 da suka ji rauni.
Wannan lamari cewar masana sha’anin taro irinsu Moussa Aksar ke ganinsa tamkar wani yunkurin mai da hannun agogo baya ne ga shirin kafa cibiyar tsaron Faransan a wannan yanki.
Sakataren kungiyar RJPS mai ayyukan fadakarwa akan sha’anin tsaro da zaman lafiya Souley Mage na ganin bukatar duba tsarin bayar da bayanai a tsakanin sojon cikin gida da na kasashen dake da sansani a yankin sahel.
Matsalar tsaro a kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso wani abu ne da ya zama wajibi a yi waiwaye don magance wasu kurakuran da aka yi a can baya Inji Aksar Moussa.
Wannan shi ne hari na 5 da ‘yan ta’adda ke kai wa a yankin Tilabery a cikin watan Yulin da ya gabata inda aka yi asarar rayukan gomman fararen hula akasari wadanda ake riskewa a gonakinsu duk da irin matakan da hukumomi ke cewa suna dauka don kawo karshen wannan al’amari da ke kara bullowa da sabbin kamani a kulliyaumin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: