Shugaban Rasha Vladimir Putin ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar da gagarumin rinjaye, lamarin da zai ba shi wani karin wa'adi na mulki.
A bikin karramawa na Academy karo na 96 na wannan shekara an ga jarumai a cikin fita ta kece raini da tufafi iri daban-daban da ke kyalkyali da daukar ido.
An bude gasar League ta kwallon Kwando ta nahiyar Afirka a ranar Assabar, a dandalin wasanni na SunBet da ke birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu, inda kungiyoyi 4 daga nahiyar za su fafata wasanni 22 a kashin farko na gasar da ake kira Kalahari Conference.
Rikicin siyasa da karuwar tashe-tashen hankula a Haiti sun haifar da yanayi mai wahalar magancewa ga al'ummar Haiti.
A ranar Alhamis ne wasu bata-gari suka yi wa wasu dakarun soji kisan gilla lokacin da suke kokarin sulhunta rikici tsakanin kabilar Okuama da Okoloba a Jihar Delta.
A birnin Mogadishu babban birnin kasar Somalia mai fama da rikice-rikice, dattawa kan tattaru a kowace rana a gundumar Bondere, domin gasar harbin kibau. Gasar dai wani sashe ne na al’adun kasar masu dadadden tarihi.
Wani mai sana’ar POS a Unguwar Kurnar Asabe da ke Jihar Kano ya mayar da kusan naira miliyan 10 da wani kwastomansa ya yi kuskuren tura masa a maimakon dubu 10.
Paul Alexander ya rasu ranar Litinin yana da shekaru 78, a cewar wata sanarwa da dan'uwansa, Philip Alexander, ya fitar ta kafar sada zumunta.
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama mutane 11 da suka hada da mata daya da maza goma saboda laifin cin abinci da rana tsaka a bainar jama’a cikin watan Ramadan a jihar.
Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta ce za su kama 'yan kasar da ke yaki da sojojin Isra'ila ko kuma tare da su a Gaza idan sun komo gida.
Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da dalibai da ma’aikata 286 a wata makaranta a arewacin Najeriya a makon da ya gabata, sun bukaci jimillar Naira biliyan 1, kwatankwacin dalar Amurka 620,432 domin a sako su.
Hukumar Baitulmalin Amurka ta kakaba takunkumi ma mutane da hukumomi 16 a yankunan kuryar Afirka da Gabas ta Tsakiya.
Yadda kungiyoyin 'yan bindiga ke samun garkuwa da mata da yara a sauwwake, musamman a arewacin Najeriya, na kara ta'zzara da kuma tayar da hankali.
Zuwa ranar Litinin, rana ta 3 a jere, haramcin kamfanin hada hadar kudi na Binance na aiki.
Domin Kari