Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Sana'ar POS a Kano Ya Mayar Da Naira Miliyan 10 Da Aka Tura Masa


Mai Sana'ar POS a Kano
Mai Sana'ar POS a Kano

Wani mai sana’ar POS a Unguwar Kurnar Asabe da ke Jihar Kano ya mayar da kusan naira miliyan 10 da wani kwastomansa ya yi kuskuren tura masa a maimakon dubu 10.

Lamarin dai ya faru ne yayin da abokin kasuwancinsa ya yi yunkurin tura wa mai POS din naira dubu 10, kamar yadda rundanar ’yan sanda Kanon ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne tun a watan Disamba na shekarar 2023, lokacin da mai sana’ar POS mai suna Mohammed Sani Abdulrahman ya fahimci cewa wani kwastomansa wanda ya karbi naira dubu 10 daga wurinsa ya tura masa naira miliyan 10 bisa kuskure.

Daga nan ne sai mai POS din mai shekaru 37 ya garzaya hedikwatar ’yan sandan Kanon ya sanar da su abin da ya faru.

Sanarwar da Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce sun kwashe kimanin wata uku suna bincike kafin su gano mutumin wanda dan kasuwa ne a Kasuwar Dawanau da ke Kano.

Rundunar ’yan sandan ta ce tuni mai POS din ya mayar wa kwastoman kudinsa naira miliyan tara da dubu dari tara da casa’in.

Sai dai jin dadin haka ya sa dan kasuwar ya ba mai POS din kyautar naira 500,000.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Usaini Gumel ya yabawa Sani mai POS bisa gaskiya da amana da ya nuna a harkar kasuwancinsa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG