Hukumar dai na zarginsu da badda sawun wasu kudade don turawa ma kungiyar Al-Shabaab mai tsattsauran ra'ayin addini..
Hukumar Baitulmalin ta ce "hadakar ta attajiran kamfanoni" wani bangaren yanar intanet ne na tara kudade da kuma batar da sawunsu don amfanar ƙungiyar mai alaƙa da Al-Ka'ida wadda ke harkokinta a Somaliya.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ce kamfanonin da aka kakaba wa takunkumin sun hada da Fintech Haleel Commodities LLC da ke Dubai wanda kuma ke da reshe a Kenya, da Somalia, da Uganda, da kuma Cyprus.
Qemat Al Najah General Trading mai hedikwata a Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda "wani jigo ne ga hadakar ta wajen badda sawun kudade," da kuma wani kamfanin bas na Kenya da ke tallafa wa Al-Shabaab ta fuskar harkokinta wanda shi ma an kakaba masa takunkumi.
Hukumar Baitulmalin ta ce Al-Shabaab na samun sama da dala miliyan 100 a duk shekara ta wajen tursasa wa kamfanoni da daidaikun mutane, da kuma tallafin kudi na ‘yan kasuwa masu alaka da su.
Dandalin Mu Tattauna