Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Haramcin Kamfanin Binance Na Nan Daram


Kamfanin Binance
Kamfanin Binance

Zuwa ranar Litinin, rana ta 3 a jere, haramcin kamfanin hada hadar kudi na Binance na aiki.

Matakan da hukumomi suka dauka na bayan nan na zuwa ne bayan yunkurin ganin an ceto darajar naira da shawo kan matsalolin tattalin arzikin kasar.

Hukumomi sun ce Binance ya sauya akalar farashin hada-hadar kudade ta yin hasashe da kuma sanya farashi, lamarin da ya haifar da faduwar darajar naira.

Gwamnatin kasar ta kuma zargi kamfanin da daukan nauyin ayyukan ta’addanci, da yin sama da fadi da kudin gwamnati inda ta ayyana wata hada-hadar dala biliyan $26 da aka yi ta wannan kafar wanda aka kasa gano su. Zargin na cikin wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na yanar gizo a karshen watan jiya, Binance ya musa aikata laifi.

Illustration shows representations of cryptocurrency Binance
Illustration shows representations of cryptocurrency Binance

Masani kan harkokin tattalin arziki Isaac Botti, ya ce hada-hadar kudi ta kamfanin Binance ba ita ce tushen matsalolin tattalin arzikin da Najeriya ta ke fuskanta ba.

Abin da ya haifar da wannan yanayi shi ne yadda muke so da kuma amfani da kudaden ketare a cikin gida Najeriya. Ba yawan kudaden da mutane su ke ajiyewa a asusun Crpto ne babban kalubalen ba. Yawan dalar da babban bankin Najeriya CBN ya sake a a kasuwa shi ne Kalubalen.

Najeriya tana da masu asusun crypto fiye da duk wata kasa a nahiyar Afirka, jumlar sama da mutum miliyan 13, sai kuma Kenya wacce take biye da ita da mutum miliyan 4.4.

Shugaban Binance Changpeng Zhao
Shugaban Binance Changpeng Zhao

Cikin wata sanarwar da ya fitar a makon da ya gabata, kamfanin Binance ya ce zai mai da duk wani kudi da ya rage a kafar zuwa tetha- wasu sulallan kudin crypto da darajar ko wani guda ya kai dalar Amurka guda.

A bara, Najeriya ta kaddamar da wasu dabarun samar da daidaito sannan ta soke bada tallafin mai da zummar farfado da tattalin arzikin kasar. Sai dai bayan daukan wadannan matakan, darajar nairar ta yi faduwar da ba a taba gani ba. Masharhanta sun ce haramta mu’amala da Binance da gwamnati ta yi zai sa mutane su rasa ayyukan su.

Kwararre a harkar hada-hadar kudade Jahhel Chidi ya yi na’am da wannan matakin amma ya ce ‘yan Najeriya za su koma mu’amala da wani nau’in crypto wanda zai cike gibin da daina amfani da Binance ya haifar.

“Abin da wannan zai haifar shi ne mutane za su koma wani tsarin hada-hadar kudaden, mutane su na da zabin hada hada da wasu nau’ukan crypto da ake samu akan dandalin Binance.”

A watan Fabrairu, hukumomi a Najeriya sun far ma kamfanonin hada hadar kudi na cikin gida sannan suka soke lasisin kamfanoni sama da 4,000 bayan da darajar naira ta fadi inda ake canja kowace dala daya akan naira 1,900.

Chidi ya ce ya zama wajibi gwmanatin Najeriya ta lalubo matakin shawo kan kalubalolin matsalar hada-hadar kudaden ketare a kasar.

Ina ganin, an yi gaugawar daukan wannan matakin ba tare da an gudanar da kwakkwaran bincike a game da zargin da ake yi na irin rawar da Binance ya taka wajen hauhawar farashin canja dala zuwa naira ba. Babban abin da ya kamata nake gani ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta mai da hankali kan kudin da ake biya na shigo da kaya daga ketare domin ya taka rawa wajen faduwar darajar naira. Binance ne dai ya fuskanci fushin gurguwar fahimtar gwamnati.

A shekarar da ta gabata, babban bankin Najeriya ya janye haramcin da ya yi ma kamfanoni masu hada-hadar kudade na crypto inda ya ba su izinin gudanar da harkokinsu, matakin da ake gani ya dace wajen karfafa darajar kudaden digital.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG