Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Putin Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Rasha


Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar da gagarumin rinjaye, lamarin da zai ba shi wani karin wa'adi na mulki.

Rasha ta bada sanarwar cewa shugaba Vladimir Putin ne ke kan gaba da kaso 88% na yawan kuri’un da aka kidaya a zaben shugaban kasar da ya gudana ranar Lahadi, zaben da bai ba masu kada kuri’a wata sahihiyar damar zaben ra’ayinsu ba, yayin da shugaba mai yin komai dole ke bibiyar mutanen da basa ra’ayinsa.

Zaben na wuni 3 wanda aka fara a ranar Jumma’a, zai bai wa Putin damar tsawaita wa’adin mulkin shi na shekaru 24 da karin wasu shekaru 6. Zaben ya gudana cikin wani yanayi na takura inda babu damar kalubalantar Putin.

Fadar White House ta Amurka ta caccaki sakamakon zaben tare da bayyana cewa an gudanar da zaben ba tare da 'yan hamayya ba, ganin cewa daukacin masu adawa da Shugaba Putin na tsare a gidan yari.

Babban abokin hamayyar Putin Alexy Navalny ya mutu a wani gidan kaso a watan Fabrairu, sannan sauran masu adawa da shi suna tsare a gidan yari ko kuma sun boye a kasashen waje.

Alexei Nevalny
Alexei Nevalny

Don nuna goyon bayansu ga bukatar siyasar Navalny ta karshe, masu kada kuri’a sun yi dafifi a rumfunan zabe a manyan biranen kasar da tsakar rana don kada kuri’un su don tumbuke Putin, duk da cewa babu wani tasiri da zaben nasu zai yi.

Putin mai shekaru 71 a duniya, sakamakon wannan zaben zai ba shi damar ci gaba da rike madafun iko a wani sabon wa'adi na shekaru shida.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG