Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Bukaci Dala 620,000 Domin Sako Mutanen Da Aka Yi Garkuwa Da Su


Yan Bindiga
Yan Bindiga

Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da dalibai da ma’aikata 286 a wata makaranta a arewacin Najeriya a makon da ya gabata, sun bukaci jimillar Naira biliyan 1, kwatankwacin dalar Amurka 620,432 domin a sako su.

Kakakin iyalan wadanda aka yi garkuwa da su kuma wani dan majalisar karamar hukumar ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A ranar 7 ga watan Maris ne aka sace yaran makarantar da wasu manyan dalibai da kuma wasu ma’aikatan makarantar a garin Kuriga da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya, wanda shi ne karon farko da aka yi garkuwa da mutane da dama a kasar tun shekarar 2021.

Jubril Aminu, shugaban al’ummar da ke aiki a matsayin mai magana da yawun iyalan wadanda aka yi garkuwa da su, ya ce masu garkuwan sun kira shi ta wayar tarho ranar Talata.

Masu garkuwa da mutane
Masu garkuwa da mutane

“Sun bukaci jimillar naira biliyan daya na kudin fansa ga daukacin dalibai da ma’aikatan makarantar,” in ji Aminu.

"Sun ba da wa'adin biyan kudin fansa cikin kwanaki 20, daga ranar da aka yi garkuwa da su, sun ce za su kashe dukkan daliban da ma'aikata idan har ba a biya bukatar kudin fansa ba."

“Eh, masu garkuwa da mutane sun kira al’umma ta lambar Jubril Aminu, suka kuma gabatar da bukatar,” inji shi.

Ibrahim ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "Sun kira ta ne daga wata lamba da aka sakaye ta amma hukumomi na kokarin gano lambar."

Ya kara da cewa jami’an tsaro na daukar kwararan matakai domin ganin an sako daliban.

Jami'in yada labarai da hulda da jama'a na gwamnmatin jihar Kaduna, Samuel Aruwan
Jami'in yada labarai da hulda da jama'a na gwamnmatin jihar Kaduna, Samuel Aruwan

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, bai amsa bukatar neman karin bayani da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi nan take ba game da bukatun masu garkuwa da mutanen.

Su ma masu magana da yawun shugaban kasa Bola Tinubu da sojojin kasar ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba.

Ministan yada labaran kasar, Mohammed Idris, ya shaidawa manema labarai a ranar Laraba cewa, matsayar Tinubu kan sace-sacen da aka yi a Kuriga shi ne jami’an tsaro su tabbatar da sako mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutanen ba.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu

"Shugaban kasa ya ba da umarnin cewa dole ne jami'an tsaro su tabbatar da cewa an dawo da wadannan yaran da duk wadanda aka yi garkuwa da su lafiya cikin gaggawa sannan kuma a kan haka su tabbatar ba a biya ko sisin kwabo domin kudin fansa ba."

A karkashin magabacin Tinubu, an bullo da wata doka ta kulle duk wanda aka samu yana biyan kudin fansa don sako wanda aka yi garkuwa da su a gidan yari, a daidai lokacin garkuwa da mutane a Najeriya ya zama ruwan dare.

Bukatar kudin fansar daliban Kuriga da ma’aikatan makarantar, ya kai sama da dala 2,000 kan kowanne mutum daya, ko kuma fiye da kudin shiga na kowani kowani shekara a Najeriya, a cewar bayanan asusun lamuni na duniya. ($1 = 1,611.7800 naira)

~ REUTERS

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG