A ziyarar da Yan majalissun Tarayyar Najeriya suka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari a fadar sa ya nuna rashin jin dadin goyon bayan da basu bashi ba a wa'adin mulkinsa na farko.
Majalisar dokokin Tarrayar Najeriya ta umaurci dukkanni ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu su cire dokar kayyade shekaru wajen daukar ma'aikata aiki a fadin Najeirya.
Rundunar Yan Sandan Najeriya tare da hadin gwiwar wata kungiya da ake kira da Operation Forest Storm, sun samu nasarar kama wasu mutane da ake zargi cewa, 'yan ta'adda ne a jihar Taraba.
Masana sun yi kira ga Shuwagabanni Kano da su Hada Kai domin Inganta Rayuwar Al'ummar Jihar mai makon abunda zai haifar da rikici.
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya gudanar da wani zaman tattaunawa kan rikicin dake faruwa a kasar Kamaru a ‘karon farko.
Masu gabatar da kara a Sudan sun tuhumi tsohon shugaban kasar Sudan, Omar Al-Bashir da hannu a kisan masu zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.
Kasar Saudi Arabia tace tankokinta biyu sun yi mumunar lalacewa a wani harin ganganci da aka kai da safiyar shekaranjiya Lahadi a gabar tekun Hadaddiyar Daular Larabawa. Sai dai ba a bada wani karin bayani a kan lalacewar ba.
Kasar China tace zata kakaba Haraji na dala biliyan sittin a kan kayan Amurka, da ake shiga da su kasar ta.
Jami'iyar APC a jihar Adamawa taki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa a jihar da ya bayyana dan takarar PDP Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe kuru'u masu yawa a jihar, lamarin da ya haddasa rikici tsakanin shugabannin APC a jihar ta Adamawa.
Hotunana Shugaba Muhammadu Buhari da mukarraban sa a offishin kamfen din jam'iyar APC dake garin Abuja, yayin da ya isa domin yaji abunda ke wakana akan sakamokon zaben shugaba kasa,
Hukumar EFCC shiyyar arewa maso gabas mai shelkwatar a garin Gombe ta kama shugaban karamar hukumar Dukku tare da kansila da suke jihar Gombe bisa laifin sayen kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a yau Asabar 23 ga watan Faburairu 2019.
Dimbin magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma dan takarar shugaban kasa a jami'iyyar APC sun bayyana matukar farin cikin su da nasara ya yi a mazabar abokin karawarsa dan takarar PDP Atiku ABubakar.
An kammal babban zaben Najeriya da aka gudana a yau 23 ga watan Faburairun shekarar 2019, cikin lumana a babban birnin tarayya inda manyan ‘yan takara ke da dimbin magoya baya.
A Jihohin Kano da Jigawa An samu isar Jami’ai da kayayyakin zabe da wuri a wasu mazabu na yankunan jihohin.
Jam'iyyar mai mulki ta kasar Uganda ta amince da shugaban kasar Yoweri Museveni a matsayin dan takara a zabe mai zuwa na shekarar 2021.
A yau Talata ne shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar plato, ya tabbatar da cewa za'a gudunar da zaben 2019 a garin Quanpa, bayan offishin hukumar ya kama da wuta ya yin da wasu katunan mutane da kayan aiki suka kone.
Bayanai sun yi nuni da cewa amfani da wayar salula akan aiki na daga cikin dalilan dake haifar da rashin samun cikakiyar nutsuwa a wajen jami’an tsaro.
Shugabannin wakilan da ke sa ido kan zaben Najeriya na kasa da kasa, tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya, sun rarrashi ‘yan Najeriya kan dage babban zaben kasar da hukumar zabe ta INEC ta yi
Domin Kari