Cikin kwanakinan masu satar mutane suna garkuwa da su domin neman kudin fansa na cin karensu babu babbaka a kauyuka da birane.
Domin magance wannan matsalar ce, yasa rundunan yan sandan Najeriya tare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro,suka kaddamar da rundunan hadin gwiwa mai aiki da cikawa mai taken Operation Forest Storm, shirin da ya soma samun nasara a jihar Taraba inda aka cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
CP Alkasim Sanusi dake zama kwamishinan yan sandan jihar Taraba yace yanzu haka sun sami nasarar cafke wasu da ake zargi mutum 49,inda yayi karin haske da cewa.
To ko me al'umman jihar ke cewa kan wannan matsalar dake hana jama'a barci a yanzu?
A makwabciyar jihar Taraba kuwa wato jihar Adamawa, rahotanni da kuma al'umman Madagali da Michika ne suka tabbatar da cewa mayakan Boko Haram sun kai wani sabon hari a Shuwa, cikin dare,wanda kawo yanzu ba'a tantance irin barnar da suka yi ba, yayin da Jami' an tsaro ke cewa an samu nasarar fatattakarsu .
Ga Ibrahim Abdula'aziz dauke da Rihotton cikin sauti.
Facebook Forum