Jam'iyya mai mulki ta kasar Uganda ta amince da shugaban kasar Yoweri Museveni a matsayin dan takara a zabe mai zuwa na shekarar 2021.
Jam’iyyar NRM ta kasar tayi wannan shawarar ne na zaben Museveni mai shekaru 74, bayan da a shekara ta 2017 majalisar dokokin kasar ta amince da kawarda dokar kayyade shekarun ‘yan takara zuwa shekaru 75, wadda Kundun Tsarin Mulki ta Kasar Uganda ta amince da shi a watan Yulin bara.
Wannan shine karo na biyu Kenan da majalisar dokokin ta kasar, wacce ‘yan jam’iyyar NRM suka mamaye, ta canja tsarin mulkin Uganda don baiwa shugaba Museveni damar yayi tazarce, bayan da aka kawar da tanadin kayyade tsawon mulki shigaban kasa ga wa’adodi biyu.
Shi dai shugaba Museveni tun shekarar 1986 yake kan karagar mulkin Uganda.
Facebook Forum