Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Hana Kayyade Shekaru A Daukar Aiki


Majalisar dokokin Tarrayar Najeriya ta umaurci dukkanni ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu su cire dokar kayyade shekaru wajen daukar ma'aikata aiki a fadin Najeirya.

Biyo bayan koke koke da 'yan Najeriya ke yi kan yadda wadansu ma’aikatun gwamnati ke sanya dokar kayyade shekaru wajen daukan ma'aikata aiki, Majalisar tarraya Najeriya ta saka dokar hana kayyade shekaru wajen daukar aiki.

Onorabil Timothy Ngolu Simon, Daya daga cikin yan majalisa da suka amince da dokar,yace daya daga cikin dalilaan da yasa Majalisa ta ce a cire wa'adin shekaru a mai’aikatun gwamnati da suke so su dauki ma'aikata aiki shine, akwai alamun ana bin son zuciya kuma ana karya doka wajen kin daukan 'ya'yan talakawa aiki.

Onorabil Ngolu, shi kuma cewa ya yi akan kayyade shekaru a lokacin daukan 'yan sanda da sojoji wanda zai sa a zubar da matasa mararsa karfi da dama amma bai kamata ace an kayyade shekaru a dukkan Ma’aikatun gwamnati ba.

Fatima Ahmed Musa matashiya ce da ta kamalla karatun Jam'i'a da jimawa kuma tana ta neman aiki ba ta samu ba, ta ce cire wanan wa'adi yayi mata dadi,saboda zai ba matasa dama su samu ayyuka da suke so, su ma a dama da su har su zama abin alfahari.

To sai dai Sanata Ahmed Babba Kaita ya ce yana ganin dokar ta sabawa hankali saboda zai ci karo da abubuwa da dama, kuma ba za ta yi tasiri a ma'aikatun yan kasuwa ba, saboda su kan nemi masu yawan shekaru ne da kuma kwarewa saboda suna aiki ne na kasuwanci domin samun kudi,kuma ba za a ce sai dai su dauki mai karamin shekaru ba.

Saurari Rahotton Medina Dauda cikin Sauti..

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG