Mai Magana da yawun hukumar zabe na jihar, Mallam Bello Bajoga ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Abdulwahab Muhammada ta wayar tarho.
Mallam Bello Bajoga yace ganin irin abubuwa da suka faru a baya, hukumar ta bukaci duk wanda ya samu labaran suka shafin sayen kuri’a ko dillancin sa ko kuma bada toshiyar baki ya kawo mata, domin daukar mataki da ya dace a kan duk wanda aka same shi da aikata wannan laifi.
Ya kara da cewa a yau da ake zabe ne aka kira jami’an hukumar aka tsegunta musu cewa wasu na sayar da kuri’a, yace jami’an nasu basu yi kasa a gwiwa ba suke je garin da ake wannan aiki. Mallam Bello ya fadawa Muryar Amurka cewa jmi’an hukumar zaben sun kama mutanen dumu-dumu suna wannan danyen aiki.
Yace tuni sun kama kasilar da ake zargin sa da bada kudi kana sun gayyaci shugaban karamar Dukku da ake sayar da kuri’ar kuma suna tsare a hannun hukuma domin gudanar da bincike a kan alakar su da kuma rawar da suka taka a wannan abu.
Bello Bajoga yace akwai wasu kame-kame da suka yi a jihar Gombe da baki dayan shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.
Ga hirar Abdulwahab Mohammed ya yi da mai Magana da yawun hukumar INEC a Gombe:
Facebook Forum