Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Zabe Cikin Lumana A Abuja


Jama’a sun fara kada kuri’ar zaben shekarar 2019 a unguwar Wuse 2 dake birnin tarayya Abuja.
Jama’a sun fara kada kuri’ar zaben shekarar 2019 a unguwar Wuse 2 dake birnin tarayya Abuja.

An kammal babban zaben Najeriya da aka gudana a yau 23 ga watan Faburairun shekarar 2019, cikin lumana a babban birnin tarayya inda manyan ‘yan takara ke da dimbin magoya baya.

Zabe ya gudana a babban birnin Najeriya Abuja cikin lumana inda mutane maza da mata su ka fito don kada kuru’unsu tun bude runfunan zabe da yawanci a ka fara daga ka’idar karfe 8 na safe.

Masu zaben sun fi mai da hankali ne a kan manyan ‘yan takara biyu da suka hada da Muhammadu Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDP, shi ko wakilin jami'iyyar ADC a mazabar Wuse 2, ya ce dan takararsu Dr.Obadiah Mailafiya ba zai yi tasiri ba don bai yi kamfen ba.

Wasu masu kada kuri’a da suka kammala zabe, sun ce suna fatar gwanayensu zasu yi nasara.

A dakin nazarin zaben na cibiyar dimokradiyya ta Afrika, Dr.Kole Shettima ya bayyana abun da su ka lura da shi da ba kalubale mai yawa.

Bayan kammala zaben, hankali zai koma babban dakin taro

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG