Kafin isar 'yan ci-ranin a arewacin Nijar sun tagayyara a kasar Libya ciki har da mata da ƙananan yara sama da 100, inda kungiyoyin ayyukan jin kai suka nuna damuwa game da 'yan Najeriya tare da yin kira ga hukumonin Nijar da su gaggauta daukar matakan daukar nauyin wadannan mutane.
Akalla mutum 20 ne suka mutu bayan da wani kwale-kwalen katako ya kama da wuta bayan ya yi bindiga a wani kogi a jihar Bayelsa da ke gabar tekun Najeriya a ranar Laraba, in ji kakakin 'yan sandan.
'Yan sanda sun yi ta jefa barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar neman shugaban kasar ya yi murabus a babban birnin Kenya a ranar Alhamis yayin da aka rantsar da sabuwar majalisar ministocin kasar.
A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yanke huldar diflomasiyya da Ukraine saboda kalaman da jami'ai suka ce sun nuna goyon bayan Ukraine ga kungiyoyin da ke fada a makwabciyarta Mali da suka kashe sojoji da dama da mayakan Wagner na Rasha a watan Yuli.
Mutum biyar da ke cikin wani jirgi mai saukar ungulu sun mutu a wasu tsaunuka da ke arewa maso yammacin babban birnin Nepal a cewar hukumomi.
Hakan na zuwa ne bayan da kungiyar Hezbollah ta kai wasu jerin hare-haren ta sama kan Isra’ila da jirage mara matuki.
Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan yadda matasa ke tashe-tashen hankula sakamakon rashin aikin yi, inda ya yi fargabar cewa Najeriya na zaune ne a kan abin fashewa
Domin Kari