Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-zanga A Kenya Na Ci Gaba Da Kira Ga Shugaba Ruto Ya Yi Murabus


Nairobi, Kenya
Nairobi, Kenya

'Yan sanda sun yi ta jefa barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar neman shugaban kasar ya yi murabus a babban birnin Kenya a ranar Alhamis yayin da aka rantsar da sabuwar majalisar ministocin kasar.

Masu fafutuka ne suka shirya zanga-zangar a birnin Nairobi bayan da shugaba William Ruto ya kori kusan dukkanin ministocinsa tare da kara 'yan adawa a cikin abin da ya kira gwamnati mai cikakken tsari.

An rufe harkokin kasuwanci a birnin kuma motocin sufurin jama'a sun kasance daga tsakiyar yankin kasuwanci inda suka saba.

'Yan sanda sun kuma sanya shingaye a kan hanyoyin shiga birnin.

KENYA
KENYA

Ofishin shugaban kasar, inda aka rantsar da sabbin ministocin a safiyar ranar Alhamis, shi ma dai an killace shi.

Manyan garuruwa ciki har da birnin Kisumu da ke gefen tafkin, tungar 'yan adawa da a baya aka gudanar da zanga-zangar ya kasance cikin kwanciyar hankali inda wasu mazauna yankin suka shaida wa manema labarai cewa ba sa zanga-zangar ne saboda an shigar da 'yan adawa cikin sabuwar majalisar ministocin kasar.

KENYA
KENYA

Kungiyoyin fararen hula, tare da kungiyar lauyoyin Kenya, sun yi kira a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa don tabbatar da hakkin ‘dan adam a yayin zanga-zangar tare da yin kira ga 'yan sanda da su guji tura 'yan sandan da ba su da bayanan sirri da kuma amfani da motocin da ba a sani ba.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG