Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Financial Times wanda gidan Talabijin na Channels ya bibiya.
“Matasanmu suna cikin tashin hankali. Kuma suna cikin tashin hankali ne saboda ba su da fasaha. Ba su da ƙarfi. Ba su da aikin yi. Dukanmu muna zaune a kan wani abu da zai iya fashewa. Kuma addu’ata ita ce mu yi abin da ya dace kafin lokaci ya kure,” ya yi gargadin.
Kalaman na Obasanjo na zuwa yayin da ake zanga-zangar #Endbadgovnance da ke gudana a duk fadin kasar da matasa suka yi kan yunwa da kuncin rayuwa a kasar.
Tun a ranar 1 ga watan Agusta ne dai matasa a fadin kasar suka fara zanga-zanga.
Da yake karin haske, Obasanjo ya ce da tattalin arzikin Najeriya zai yi kyau matuka idan ba a dogara ga samar da danyen mai kawai ba.
Ya bayyana dogaro da danyen man da kasar ke yi a matsayin "mummunan kuskure". “Na yi imani mun tafka babban kuskure ta hanyar sanya ƙwayayenmu duka a cikin kwando ɗaya ta hanyar dogaro da mai. Muna da kaya masu muhimmanci, iskar gas, amma ba ma duban su,” in ji shi.
Akwai kuma gazawar Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), Kamfanonin Mai na duniya, da sauran kamfanonin mai na kasa wajen inganta hako mai domin biyan bukatun kasar.
Obasanjo ya ce Najeriya za ta iya zuba jari sosai a harkar noma mai makon kawai danyen mai.
"Amma mun yi watsi da harkar noma wacce za ta iya iya zama jigon jarinmu."
Dandalin Mu Tattauna