Kasar Nijar a duk rana ta na fama da kwararar bakin haure daga arewacin kasar musanman wadanda ake korowa daga Aljeriya.
An dai ce jami’ai sun balle kofar wani gidan da wasu mutanen suke zaune tare da tafiya da su bayan kuwa kowannen su suna cikin gida sun shafe shekaru a kasar ta Libiya.
Suka ce jami’an sun kwace duk wasu shaidu dake tabbatar da zaman su a kasar sannan kuma suka tsare su tare da mata kafin daga bisani suka jefa su cikin mutanen da aka tilasta musu fita kasar.
kungiyoyin kare hakkin bil’adama na ganin akwai bukatar gwamnatocin kasashen yankin Afirka ta Yamma da su tura wata tawaga ta jami’ai domin tattauna yadda za’a bullo ma lamarin musamman tunda akwai dangantaka mai kyau tsakanin kasar Libiya da wasu kasashen na Afirka irin su Najeriya da Nijar.
To saidai wadanda aka koro na fatan samun ayyukan yi a kasashen su domin acewar su rashin aikin yi ne ke sanya su wadannan tafiye tafiyen zuwa wasu kasashen
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna