Wannan mataki na zuwa ne shekaru 13 bayan da gwamnatin Najeriyar ta jingine koyar da darasin tarihi a duk fadin kasar.
Bayanan Babban Bankin Najeriya na nuni da cewa, an kashe sama da Naira biliyan uku da rabi kan harkokin ilimi a kasashen ketare tun daga shekarar 2015 da gwamnatin Muhammadu Buhari ta hau kan karagar Mulki zuwa wannan shekara da muke ciki ta 2022.
Yanzu haka dai jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS tare da hadin kan jami’a hukumar kwana-kwana da ayyukan ceton gaggawa a jihar Legas na aiki ba dare ba rana tun a jiya Alhamis, domin gano wata mata da ta fada gadar da ake kira third mainland bridge.
Hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi a Najeriya ta kama kwayoyin Tramadol da kudinsu ya kai na fiye da Naira biliyan takwas da miliyan dari takwas da sittin da daya.
A wata kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a Badagary na Jihar Legas a Najeriya an kona hodar iblis da nauyin ta ya kai na ton daya da digo 8.
Hukumar NDLEA mai yaki da safaran miyagun kwayoyi ta Najeriua ta kama wasu masu safaran muggan kwayoyi da hodar iblis ko cocaine da yawansa ya kai na tan 1.8, ko kwatankwacin kilogram 1855 a birnin Lagos.
Yayin da wa’adin ranar 31 ga watan Yuli na rajistan katin zabe na dindindin (PVC) ke kara kusantowa gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, ya amince da wa’adin kwanaki hudu na hutu ga ma’aikata a jihar domin su samu katin zabe.
Shugabannin Al'uman yankin Arewacin Najeriya da wasu sarakunan yankin Yammacin kasar, sunyi kira ga hukumomin tsaron Najeriya da su tashi tsaye wajen tabbatar da tsaro kafin zaben shekara ta 2023 mai zuwa a wasu taruka daban daban da suka gudanar a birnin Legas.
Wata babbar kotun jihar legas ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wani dan asalin kasar Denmark da aka samu da laifin kashe matarsa da diyarsa 'yar shekaru 3 da rabi.
Gwamnatin Amurka zata kashe zunzurutun kudi har dalar Amurka miliyan $537, wajen gina ofishin jakadancinta mafi girma a duniya.
A yayin da masu neman takarar shugabancin Najeriya a tutar jam'iyar APC mai mulki ya haura 20, 'yan takarar neman shugaban kasa a tutar APC daga yankin yarbawa sun gudanar da taro a Legas tare da jaddada bukatar ganin 'dan yankin ne ya lashe zaben kasa a shekara mai zuwa.
Domin Kari