Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: An Yi Taron Hada Kan 'Yan Takarar Shugaban Kasa Na APC


Farfesa Yemi Osinbajo na gaisawa da Senator Bola Ahmed Tinubu tsohon Gwamnan Legas, Gwamnan legas Babajide Sanwolu ne a tsakiya.
Farfesa Yemi Osinbajo na gaisawa da Senator Bola Ahmed Tinubu tsohon Gwamnan Legas, Gwamnan legas Babajide Sanwolu ne a tsakiya.

A yayin da masu neman takarar shugabancin Najeriya a tutar jam'iyar APC mai mulki ya haura 20, 'yan takarar neman shugaban kasa a tutar  APC daga yankin yarbawa sun gudanar da taro a Legas tare da jaddada bukatar ganin 'dan yankin ne ya lashe zaben kasa a shekara mai zuwa.

Kodayake farashin neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya ya fi na kowani zabe tsada a tarihin Najeriya, inda na jam'iyyar APC mai mulki ma ya kai har Naira miliyan 100, hakan bai hana tarin 'yan takarar shugabancin tururuwa domin sayen takardar takarar ba. Yanzu yawansu ya kai 24 a karkashin APC kawai.

Ko a yankin yarbawa na kudu maso yanmacin Najeriya yanzu haka akwai 'yan takara da suka hada da Matainakin Shugaban Najeriya, Farfeasa Yemi Osinbanjo da Senator Bola Ahmed Tinubu da tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amuson, sai kuma tsohon shugaban majalisar Wakilai Hon. Dimeji Bankole da kuma Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, kodayake dai masu kula da harkokin siyasar yankin na ganin har yanzu Bola Tinubu ne kan kaba a tsakanin 'yan takaran, amma dai neman hadin kai tsakanin 'yan takarar abu ne da ake bukata inji tsohon shugaban Jamiyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Ondo, Bisi Akande, wanda ya jagoranci taron wanda kuma yace a karshen sa, an cimma matsaya na ganin yankin ya fito da wanda zai gaji shugaba Buhari a shekara ta 2023.

To ko yaya magoya bayan wadannan 'yan takara na yankin yarbawan ke ganin wannan taro? Babangida Mani, mai goyon bayan Tinubu, da Abubakar na Babanyawo, mai goyon bayan Fayemi Kayode, sun ce akwai bukatar marawa 'yan takaran da ya dace baya, yayin da kowannensu ke goyon bayan gwaninsa.

Saurari cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG