Bayan wannan kudade da gwamnatin ta kashe, su kansu yan kasar sun kashe biliyoyin daloli wajen biyan kudin makaranta a kasashen waje, ba tare da samun ribar wannan kudi ba na zahiri a cikin gida ba.
Irin wannan kudi dai da yan Najeriyan ke kashewa a kasashen wajen na kara karya darajar Naira akan kudin dala, inji masana tattalin arziki, wadanda suka ce kasar na fama da karancin dalar Amurka a asusunta na ketare.
Bayan wannan kuma, yawaitar yajin aikin malaman jami’o’i da na kwalejojin kimiyya da fasaha a kasar sun taimaka wajen sanya iyaye da dalibai kwadayin zuwa kasashen waje domin kammala karatun su na gaba da sakandare.
A kwanan nan ne dai kungiyar malaman jami’o’in kasar suka janye yajin aikin da suka shafe watanni fiye da 8 suna yi tare da neman gwamnati ta karawa makarantun kasar kudaden gudanarwa tare da samar da kayan aiki da kuma inganta rayuwar malamai da dalibai.