A wata sanarwa da Gwamnatin ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan, Mista Hekeem Muri-Okunola, ta ce kwanakin hutun ya fara aiki ne daga ranar 26 ga watan Yuli zuwa Juma’a 29 ga watan Yuli kafin wa’adin da hukumar zabe ta ba wa masu son kada kuri’a su ya cika.
Biyo bayan wannan sanrwa dai suma shugabanni da sarakunan aluman yankin kasar Yarbawa da Yan Arewa mazauna yankin kudu maso Yanmacin Najeriya sunyi kira ga alumomin su dasu daure suje domin rajistan katin zaben...lamar yarda Oba Oluwo na Kuta Mai Daraja ta daya Alhaji Hammed Adekunle Makama yayi kiran a madadin sauran sarakunan na kasar Yarbawa...
Yace akwai bukatar kowa da kowa yaje ya yanki katin zabe sa domin ta haka ne za'a samu sauyi bisa doka, don haka ina kira ga matasa dasu daure,suyi anfani da wannan dama domin samun katin zaben da dindindin".
Shima a bangaremsa Sarkin Fulanin Shagamu kuma mataimakin shugaban Fulanin dake kudancin Najeriya Alhaji Salisu ba shan kai kira yi ga 'yan arewa da sauran jama'a su hanzarta domin samun katin zaben, kafin hukumar zabe ta rufe a ranar 31 ga wannan wata na yuli yace Hakki ne da ya rataya a wuyan kowane ‘dar kasa ya shiga harkar zabe a kasarshi, saboda haka, ana karfafa wa dukkan jama'a kwarin rajistan zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Wani kididdiga da hukamr zaben ta fitar na nuni da cewa jihohin lagos da Kano ne ke kan gaba wajen masu katin zabe a kasar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: