Dan wasan tseren Ghana mafi sauri, Benjamin Azamati-Kwaku ya roki ‘yan kasarsa gafara a kan gazawarsa na kai ga tseren maza na mita 100 a wasan karshe a wasannin Olympic shekarar 2020.
Tobiloba Amusan ‘yar Najeriya za ta yi wasan karshen na tseren mata na mita100 da ake tsallake shingaye a wasannin Olympic a birnin Tokyo na kasar Japan a ranarLitinin, bayan da ta samu gurbin shiga wasan karshen a yau Lahadi.
Dan damben boxing Ghana Samuel Takyi ya lallasa Jean Carlos Caicedo dan kasar Ecuador ta hanyar hukuncin bai daya da alkalai suka yanke, lamarin da ya bashi damar ketarawa zuwa matsayi na gaba a gasar Olympic a birnin Tokyo.
Biles ta fice a cikin wasan baki daya bayan da ta gaza sauka kan kafafunta a lokacin wata dirar mikiya da ta yi a gasar.
Ministan matasa da wasanni na Ghana Mustapha Ussif ya yi kira ga ‘yan wasannin Ghana da suke wakiltar kasar a gasar duniya ta Olympics da su yi amfani da wannan dama da suka samu ta zuwa gasar wajen daukaka sunayensu da na kasarsu.
An gudanar da zanga-zangar adawar daure tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma daga garinsu zuwa babbar cibiyar tattalin arzikin kasar ta Johannesburg.
Dubun dubatar fararen hula a Sudan sun gudanar da tarukan gangami a Khartoum domin cika shekaru biyu da fatattakar da sojoji suka yiwa masu rajin dimokradiya, suna neman adalci ga ‘yan uwansu da aka kashe ranar 3 ga watan Yunin 2019, a fatattakar.
A jiya Litinin jami’an sojan kasar Mali suka tsare shugaban kasa da Firai Minista da kuma ministan tsaro na gwamnatin wucin gadi.
Wasu masu sharhi na ganin rashin baiwa mataimakin shugaban kasa daman rike kasar yayin da shugaban ke duba lafiyarsa a Ingila, ka iya shafar dangantakarsu.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun yi karin haske a game da juyin mulkin da dogarawan fadar shugaba Issouhou Mahamadou suka murkushe a cikin daren Talata wayewar jiya Laraba 31 ga watan Maris.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta fada a jiya Lahadi cewa jami’anta sun dakile yunkurin wasu masu garkuwa da mutane kana aka ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su.
Gwamnatin Najeriya ta yi matashiya ga hukumomin kasar game da labarin da ake yadawa kan allurar rigakafin COVID-19 na jabu da ake ce za a shigo da su a Afrika.
Kungiyar mabiya akidar Shi’a a Najeriya ta Islamic Movement in Nigeria, IMN, ta ce ‘yan Najeriya su nemi bayani daga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kan tabarbarewar tsaro a cikin kasar.
Gwamnatin jihar Legas a Najeriya ta ce ba za ta lamunta da mutane masu tafiya cibiyoyin allurar rigakafi ba tare da sun samu cancantar yin hakan ba saboda ta himmantu ne wurin tabbatar da ganin aikin rigakafin coronavirus ya yi nasara.
Damuwar da hukumomi ke yi sakamakon karuwar amfani da miyagun kwayoyi a Najeriya, ya sa hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa ta (NDLEA) ta bayyana aniyarta ta bude dakunan gwaji a jihohi 36 na tarayya.
A jamhuriyar Nijar wasu ‘yan bindiga sun kai hari a karkarar Anzourou da ke yankin Tilabery, inda rahotanni ke cewa sun kona makaranta da asibitin kauyen (Zeban) Zebane tare da hallaka mutane a kalla 7 dukkan su fararen hula
A jamhuriyar Nijar an kaddamar da zaman sabuwar Majalisar Dokokin Kasar mai wa’adin wakilcin shekaru biyar.
Bayan binciken da gwamnatin jamhuriyar Nijer ta gudanar, ta ce ‘yan ta'adda da suka fito daga kasar Mali sun kai hare hare a cikin garuruwa da dama da wata tunga a cikin gundumar Tilliya ta jihar Tahoua inda su ka kashe mutane 137 wasu da dama kuma suka jikata.
Babban kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta “Civil Defense”, Dakta Ahmed Audi, ya fada cewa kishi da hassada a tsakanin hukumomin tsaron kasar na kara ta’azzara rashin tsaro a cikin kasar.
Bayan sanar da bullar sabuwar cuta a jihar Kano a farkon wannan mako sakamakon shan lemon da ake zaton ya gurbace, hukumomi a jihar sun tashi haikan wajen daukar matakan ganin an kawar da irin wadannan lemon daga kasuwa.
Domin Kari