Faruwar lamarin ya daure wa jama’a kai a bisa la’akari da dubban sojojin gida da na waje da aka girke a iyakar Mali da Nijar da Burkina Faso da nufin yaki da ta’addanci.
Lamarin ya faru ne a wajejen karfe 5 na yammacin jiya Laraba inda wasu mutane da ke kan babura dauke da bindigogi suka yi wa kauyen Zebane da ke da’irar Anzourou a jihar Tilabery zobe, kafin daga bisani su kutsa cikin garin kamar yadda wani mazaunin karkara wanda bai so a ambaci sunansa ba ya bayyana min ta wayar tarho.
Kawo yanzu hukumomi ba su yi bayani ba akan wannan hari to amma rahotanni na cewa maharan sun kona wata makarantar boko da asibiti sannan sun kashe mutane 7.
Kisar fararen hula wani sabon salo ne da ‘yan ta’adda suka bullo da shi a ‘yan makwannin nan da nufin haddasa rikicin kabilanci a tsakanin al’umma kwatankwacin wanda ya ba su damar mamaye arewacin kasar Mali, inji mai fashin baki a kan sha’anin tsaro, Alkassoum Abdourahamane.
Hadin kan da kungiyoyin ta’adanci ke samu daga wajen wasu daidaikun mutane a cikin jama’a ya taimaka sosai wajen yaduwar ayyukan ‘yan bindiga a baki dayan yankin Tilabery.
Shugaban kungiyar Muryar Talakka “voiw des sans voix” Nassirou Saidou, na ganin ya zama wajibi hukumomi su canza dabarun yaki don tunkarar sabon salon da ‘yan ta’adda suka bullo da shi.
Harin na kauyen Zebane na faruwa ne kwanaki 3 kacal bayan wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula 137 a gundumar Tilia ta jihar Tahoua sa’ilin da wasu fatake 58 da ‘yan bindiga suka kashe a gundumar Banibangoun yankin Tilabery a tsakiyar watan da muke ciki.
Wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma ya aiko mana Karin bayani: