A yau Liinin wata kotun Afrika ta Kudu ta fara sauraren daukaka kara da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ya shigar a kan hukuncin dauri da aka yanke masa mai yawa, yayin da ake ta zanga zanga a kan hukuncin daurinsa.
A cewar kamfanin dillancin labaran Reuters, lauyoyin Zuma sun bukaci kotun ta saki Zuma mai shekaru 79 a duniya bisa dalilin cewa kotun tsarin mulkin ta yi kuskure wurin zartar da hukunci alhali bai bayyana kotu ba.
A makon da ya gabata Zuma ya gabatar da kansa a gidan yari dake gundumarsa ta KwaZulu-Natal domin fara zaman gidan yari na watanni 15 da aka yanke masa na wulaknat umarni kotu bayan da yaki bayyana ya bada bahasi gaban wani bincike na musamman a kan zarge zarge masu yawa na cin hanci da rashawa yayin mulkinsa na shekaru 9 da yak are a shekarar 2018.
Lauyoyin sun musunta cewa yana iya fadawa cikin hadarin kamuwa da COVID-19 yayin da zai zauna a gidan yari.
Zuma dai ya musunta duk zargin da ake masa kana ya ki yarda ya ba ba da hadin kai a binciken da aka fara a makwannin karshen mulkinsa.