Takyi mai shekaru 20 da haifuwa ya mamaye zagayen farko da na uku abin da kawar da shakku cewa alkalan wasan guda biyar zasu ayyana shi wanda ya yi nasara a wasan na masu nauyin kilo 52 zuwa 57 na Featheerweight.
Dan shekaru 20 ya fara fadar ne cikin kasala amma nan da nan ya murmure bayan dakiku 30 kana ya mamaye zagayen na farko, inda alkalan biyar suka bashi maki sosai.
Shima Carlos Caicedo ya dawo zagayen na biyu da kuzari mai yawa inda ya samu alkalai 4 cikin 5 da suka bashi maki sosai.
Takyi dan damben Ghana mai shekaru 20 da ya yi taka tsantsan a fafatawar kuma ya rika kai naushi masu nauyi, ya samu nasara kana ya samu damar kai ga wasan gaba na Olympic a Tokyo.
Shi ne kuma dan damben na biyu a cikin kungiyar masu damben boxing Ghana ta Black Bombers dake Tokyo da ya samu nasarar haurawa zuwa matsayi na gaba, bayan Sulemanu Tetteh da shima ya yi nasarar kai ga wasan gaba kwanaki uku da suka gabata.
Ministan matasa da wasannin na Ghana Mustapha Ussif yana cikin jami’an Ghana kalilan da aka basu damar kusanta da ‘yan wasan a ranar Litinin yayin da dan damben boxing Ghana Suleman Tetteh ya lallasa abokin karawarsa dan kasar Jamhuriyar Dominican, Marte Rodrigo, ya yi nasara a kansa.
Ministan ya gargade sauran wakilan Ghana da su dubi nasarar da Suleman Tetteh ya yi su kuma su taka rawar gani.