Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan: Masu Zanga-zangar Sun Nemi Adalci ga Yan Uwansu Da Aka Kashe Ranar Yuni 3, 2019


Masu zanga zanga a Sudan
Masu zanga zanga a Sudan

Dubun dubatar fararen hula a Sudan sun gudanar da tarukan gangami a Khartoum domin cika shekaru biyu da fatattakar da sojoji suka yiwa masu rajin dimokradiya, suna neman adalci ga ‘yan uwansu da aka kashe ranar 3 ga watan Yunin 2019, a fatattakar.

Wasu sun ce sun gaji da alkawuran da jami’an gwamnati ke yi alhali ba a cika su kana babu wanda aka kwato masa hakkinsa.

Waleed Ihab da ya fito Omdurman yace tun da rundunar tsaro suka harbi kafarsa a cikin tashin hankalin, yana fama da radadin ciwo kana babu wata diyya daga gwamnati.

Ya fadawa Shirin Muryar Amurka na South Sudan in Focus cewa, gwamnatin wucin gadin tayi rauni dan haka ta mika mulki ga wasu daban.

A watan da ya gabata ma sojojin Sudan sun kashe mutane biyu masu zanga zangar lumana kana suka jikata wasu 37 wadanda su ma suke tuna irin wannan rana a ranar 29 ga watan Azumin Ramadana.

Kila yanzu kotun laifukan yaki ta kasa da kasa dake Hague, a Netherlands itace kadai inda zasu waiwaya domin neman adalci.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG