A cewar hukumomin sun kaddamar da bincike domin zakulo dukkan masu hannu a wannan al’amari da ya wakana kwanaki 2 kacal kafin rantsar da mutumin da kotun tsarin mulkin kasa ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gabata.
A taron manema labaran da ya kira kakakin gwamnatin Nijer minista Abdourahamane Zakaria ya ce a cikin daren Talata 30 wayewar Laraba 31 ga watan Maris dakarun gwamnati sun yi nasarar murkushe wani yunkurin juyin mulki kuma an kaddamar da bincike domin gano masu hannu a wannan al’amari don gurfanar da su a gaban kuliya.
Ya ci gaba da cewa tuni mutane da dama masu alaka da wannan yunkuri suka shiga hannun hukuma yayin da aka kaddamar da farautar wasu mutanenn na daban. Gwamnatin ta ce ta yi Allah-wadai da faruwar wannan aika aika dake barazanar maida hannun agogo baya a tafarkin dimokaradiyar da kasar Nijer ta tsunduma cikinsa kaco-kam.
Karin bayani akan: Abdourahamane Zakaria, Mahamadou Issoufou, Shugaba Muhammadu Buhari, Capitaine Sani Saley Gourouza, Jamhuriyar Nijar, PNDS, Nigeria, da Najeriya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa gwamnati na jinjinawa dogarawan fadar shugaban kasa da sauran jami’an tsaro saboda jajircewarsu a yayin wannan fafatawa abin da ke nunin biyayar da suke yiwa hukumomin jamhuriyar.
A cewar hukumomin na Nijer kura ta lafa kuma su na rike da dukkan madafun iko saboda haka suka yi kiran al’umma ta ci gaba da gudanar da harkoki kamar yadda aka saba.
Koda yake hukumomi basu ambaci sunan kowa ba daga cikin wadanda suka ce sun kama a jerin wadanda ke da hannu a yunkurin juyin mulkin, masu amfani da kafafen sada zumunta na ta yada hotunan Capitaine Sani Saley Gourouza na rundunar sojan sama a matsayin shugaban sojojin da ake zargi da kitsa wannan al’amari dake wakana sa’oi kadan kafin rantsar da sabon shugaban kasa, sai dai wasu ‘yan kasa na kallon abin tamkar wani wasan kwaiwayo da aka tsara da nufin cimma wata manufar boye.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti: