Rawar gani da Azamati-Kwaku ya taka a ranar 26 ga watan Maris shekarar 2021, inda ya kashe tarihin kasa da Leo Myles-Milles ya kafa a (1988) na kamala tseren cikin dakiku 9.98, yayin da shi Azamati ya yi tseren cikin dakiku 9.97, lamarin da ya baiwa ‘yan Ghana da dama kwarin gwiwar ya kimtsa ya fafata da shahararrun ‘yan wasan duniya.
Amma tseren mita 100 da ya fara yi a Olympic a ranar Asabar shine ya zo na hudu da dakiku 10.13 a bayan wani dan wasan Australia Rohan Browning na farko da Yhan Blake na biyu da kuma dan wasan Birtabiya Chijindu Ujah
Da ya gano kuskurensa, mi gudun tseren dan shekaru 23 ya yi amfani da shafinsa na sada zumunta ya mika rokon gafararsa ga kasar Ghana baki daya.
“A yi hakuri! Gaskiya na gaza kai labari,” abin da ya rubuta a kan shafinsa kenan.
Ya ce “abubuwa zasi inganta nan gaba. Yanzu da na gano kura kurai n azan faro gyara daga wurin. Ina matukar murna da goyon baya da kuka bani. Na ji irin kaunar da kuka nuna min. Zan yi alfahari da haka kana zan yi aiki tukuru a wasannin gaba,” inji shi.
Benjamin Azamati-Kwaku zai karu da Joseph Paul Amoah da Sean Sarfo Anti da kuma Joseph Oduro Manu a wasan tsaren maza na zari-ka-ruga na mita 100 sau hudu.