A Najeriya, 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki na cece-kuce akan matakin da kakakin Majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya dauka na kin sa hannu a kasafin kudin badi har sai an biya Kungiyar Malaman Jami'o'i kudadensu,a kuma biya wadanda ‘yan sanda suka kashe shekaru 10 da suka wuce diyya.