Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Amince Da Ba Jihar California Tallafin Gaggawa


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta amince za ta ba jihar California tallafi domin taimakwa wadanda bala’in wutar daji ya shafa.

Gwamnan jihar California Gavin Newsom ne ya bayyana haka a wata takaitacciyar sanarwa bayan ya yi magana da shugaba Trump ta wayar tarho.

Yace "“Yanzu na yi waya da shugaba Donald Trump wanda ya amince da bukatar mu. Na yaba da yadda ya yarda cikin sauri,”

Gwamnan ko fadar white house basu bada cikakken bayani ba nan take akan dalilin da gwamnati ta canja matsayi yan sa’o’I bayan ya ki amincewa da bukatar tallafin na Jihar, wanda jami’ai suka ce zai samawa jihar daruruwan miliyoyin dalar Amurka.

Mai Magana da yawun fadar White House Judd Deree, tun da fari yace bukatar ta California ba’a hado da bayanai a rubuce ba da zai sa a amince kuma Trump ya yi amfani ne da shawarar da hukumar kula da agajin gaggawa FEMA wajen kin amincewar.

“ Gwamnan da shi da shugaban Jam'iyar Republican Kelvin McCarthy sun yi magana inda suka bada cikakkun hujoji da kuma dalilai na zahiri da ya sa shugaban ya amince,” inji Deere a wani jawabi bayan Trump ya canja shawara.

Dama Jihar da ta yi niyar neman a sauya kin amincewar kuma tana ganin tana da hujjan yin hakan kamar yadda Mai magana da yawun sashen bada agajin gaggawa Brian Ferguson ya fadi kafin Canja shawarar.

Newsom ya nemi tallafin ne ranar 28 ga watan Satumba sakamakon gobarar da aka yi a gundumomin Fresno, Los Angeles, Madera, Mendocin, San Bemanrdino, San Diego da Siskiyou.

Bukatar da ke kunshe a takarda mai shafi 30 ta bayanna cewa ba a kammala tantance asarar da aka tafka ba sabili da a lokacın wutar na ci.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG