Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Hana Zirga Zirga a Kagara, Jihar Neja


Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello.
Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello.

An kafa dokar hana zirga zirga na sa,o’i 24 a cikin garin kagara hedikwatar karamar hukumar Rafi ta jihar Nejan Nigeria.

Wannan dai ya faru ne bayan kisan gillar da wasu 'yan bindiga su ka yiwa wasu ‘yan banga guda 4 a wani kauyen tashar kare dake kusa da Kagaran,

Al’amarin da ya tunzura mutanen yankin suka afkawa Ofishin ‘Yan Sandan tare da kwashe bindigogi sama da guda 10.

A cikin hirarshi da Muryar Amurka, shugaban karamar hukumar Rafin, Alhaji Isma’ila Modibbo ya ce kusan kwana biyar kenan a Karamar Hukumar Rafi ake samun hare hare na ‘yan bindiga wanda ya tunzura mutanen gari suka kaiwa ‘yan sanda farmaki har suka lalata kadarori kuma suka kwace bindigogi kusa ngoma sha daya. Ya kuma bayyana cewa, an kafa dokar hana fitan ne da nufin ganin an sami kwanciyar hankali.

A nashi bayanin, kwamshinan ‘Yan Sandan jihar Nejan, Alhaji Adamu Usman, yace suna bincike akan lamari,

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti:

AN SANYA DOKAR HANA ZIRGA ZIRGA A KAGARA JIHAR NEJA
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG