Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cututtuka Da Sauro Ke Haddasawa Na Barazana A Kasar Sudan


Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Salva Kiir

MDD ta yi gargadi game da barkewar matsaloli da suka danganci kiwon lafiya a Sudan sandiyar ambaliyar ruwa wanda ya hadasa cutattuka da kwari ke haddasawa

Sama da mutun dubu 875,000 a fadin Kasar Sudan ne ruwan sama da ambaliyar ya janyo wa asarar gidajensu da amfanin gona da dabbobi masu yawa.

Ambaliyar tayi sandiyar barin kududdufai da ke tara ruwa da hayayyafar sauro, wanda ya sa ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake kula da agaji ya yi gargadin mutane miliyan 4.5 ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka da sauro ke haddasawa kamar Malariya da Chikungunya da Amosanin jinni.

Ma’aikatar Lafiya ta kasar Sudan tuni ta sanar da karuwar cutukar VHF da ya hada da zazzabin Dange, da shawara. Ma’aikatar ta sanar da wadanda suka kamu mutum 2,226 mafiya yawansu daga jihohin arewacin kasar ne tare da mutuum 56 da suka rasa rayukansu.

Mai Magana da yawun ofishin bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya, Jens Laerke yace an samu bullar Chikungunya a Dafur ta Yamma inda kusan Mutum 250 aka gano suna dauke da wannan cutar.

“Cuta mafi muni da illa ita ce Malariya. Akwai kusan mutane miliyan 1.1 da suka kamu daga karshen watan Satumbar wannan shekarar a fadin kasar. Cutar Malariya ta kai matsayin annoba a jihohi 15 daga cikin 18 na kasar.”

Laerke yace, hukumomin bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun yi tattalin kayayyaki na gaggawa da zasu bada ga wadanda suka kamu da Malariya da sauran masu bukatu na rashin lafiya. Yace kayayyakin zasu iya kaiwa ga mutane miliyan 2.7 na watanni uku. Amma ya shaidawa VOA cewa ma’aikatan agaji na shiga mawuyacin hali wajen samun kai kayayyakin wajen aiki.

Laerke Yace akwai karancin kayayyakin kula da lafiya wanda zai ci gaba da hadasa cutar daga kwari a duk fadin kasar. Ya ce ayyukan hukumar na samun matsalar kudi kuma kaso 19 na kudin da suke bukata suka samu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG