Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Kasan Najeriya Jonathan, Ba Zai Sake Tsayawa Takara Ba - Lauyoyi


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, Maris 26, 2015.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, Maris 26, 2015.

Masana kundin tsarin-mulki da shari’a na bayyana mabambantan ra’ayoyi bisa kundin tsarin mulkin Najeriya kan ko tsohon shugaba Goodluck Ebele Jonathan zai iya sake tsayawa takara, duba da yadda ya karbi rantsuwar sau biyu a bayan rasuwar tsohon shugaban kasa marigayi, Umaru Musa Yar’adua.

Barista Mainasara Kogo Umar yayi bayanin cewa sashin 130 zuwa 140 ya yi bayani akan wannan batu kan batun na cancanta tsohon shugaba Goodluck Ebele Jonathan ko zai iya sake tsayawa neman takarar shugabancin Najeriya.

Ya ce, shugaban kasa a matsayinsa na kwamandan askarawan Nijeriya, dole ne mukami ne da idan ka haushi zaka dinga nuna misalai na halayya da kima da dattaku da sanin ya kamata.

Ya kara da cewa tsarin mulkin Najeriya bashi da wani gargada akan ba za’a zabi mutun ya kasance sau biyu ba, kuma baza’a rantsar da mutuum sau biyu ba a ofis.

A kan ko an tafka kuskure a batun barin tsohon shugaba Jonathan sake neman takara a shekarar 2015, Barista Mainasara Kogo ya ce, abu ne da za’a iya kalubalanta a kotu karkashin interpretation act, doka dake zuwa tayi fashin baki tayi kuma bayani.

A 'yan kwanakin nan dai, ana danganta tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da jita-jitar zai sake tsayawa neman takara a shekarar 2023 duba da yadda ya ke kai ziyara fadar shugaban kasa a ‘yan watannin baya-bayan nan kuma manyan lauyoyi masu mukamin SAN sun yi ta yin watsi da batun, suna masu cewa idan za’a bi kundin tsarin mulki wanda aka yiwa gyarar fuska, bai cancanci sake neman takara ba.

Gyarar fuska ga kundin tsarin mulki da shugaba Buhari ya rattabawa hannu a makon jiya ya hana duk wani mataimakin shugaban kasa da ya kamalla wa’adin mulkin shugaba da ya zame ma mataimaki tsayawa takara fiye da sau daya, kazalika duk mataimakin gwamna da ya kamalla wa’adin mulkin gwamnan da ya zame ma mataimaki ma haka.

Akwai yiyuwar shugaban kasa ya kasa cika wa’adin mulkinsa a kan kujera saboda dalilai na mutuwa ko murabus, wanda kuma hakan zai bai wa mataimakinsa dama ya kamalla wa’adin mulkin kamar yadda mataimakin shugaban kasa a waccan lokaci Goodluck Jonathan, ya karbi sabuwar rantsuwar kama aiki domin kamalla wa’adin marigayi Yar’adua.

Idan dai da wannan gyarar fuska da aka yiwa dokar ta tsayawa takara na nan kuma tana aiki ka'in da na'in, a shekarar 2015, da Jonathan bai samu cancantar tsayawa sake takarar neman wani wa'adi ba.

A wani bangare kuwa, ra’ayin wasu tsaffin mataimakan gwamnoni dai ya banbanta a kan batun inda tsohon mataimakin gwamnan jihar Ogun, Sanata Adegbenga Kaka, ya ce ba su daman tsayawa neman takara sau daya tilo sabili da rike mukamin mataimakin gwamna ya sabawa tsarin mulkin demokuradiyya, yana mai cewa masu kada kuri’a ya kamata su dauki irin wannan mataki ko a yiwa kundin tsarin mulki gyaran fuska, sai tsohon mataimakin jihar Oyo, Hazeem Gbolarumi wanda ya yi maraba da dokar tare da tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, Sanata Iyiola Omisore, wanda ya yi halin ko-in-kula da dokar.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00


Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG