BAUCHI, NIGERIA - Taron na da zummar fahimtar da su game da sabbin hanyoyin gano matsalolin da ke shafar al’umma a fannin cututtuka iri daban daban, don bada rahotanni a kansu.
A taron bitar na tsawon kwanaki uku, an gayyato 'yan jarida daga gidajen radiyo guda biyu da suka hada da BRC Bauchi wanda mallakar Jiha ne, sai kuma gidan radiyon Albarka Radiyo, wanda mai zaman kansa ne, sai kuma gidan Talabijin na BATV, wanda mallakar Jihar Bauchi ne.
Kwararren dan Jarida kan sha’anin harkar kula da lafiya, kuma malami a jami’a a Jihar Legas, Declan Ohenacho, ya bayyana karfin gwiwarsa, kan irin 'yan jaridun da suka halarci taron bitar, inda ya ce an aza harsashin juyin juya hali kan yadda za a rinka bada rahotannin kiwon lafiya a Jihar.
Ya ce sakonsa ga gidajen yada labarai shi ne, su bada dukkan goyon baya wa ‘yan jarida dangane da irin ayyukan da suke son gudanarwa, domin kuwa suna da kwarrarun ma’aikata ‘yan jarida, abin da suke bukata shi ne yanayi mai kyau da goyon baya don gudanar da ayyukansu.
Jami’in da ke wakiltar, hukumar gidajen Radiyo da Telebijin na Amurka a Najeriya, Alhaji Sani Muhammed, ya yi Karin haske kan abubuwa da dama akan batun Bitar.
Mahalarta taron sun yi bayanin irin alfanun da suka samu a sakamakon halartar bitar.
Saurari rahoton Abdulwahab Muhammad: