BAUCHI, NIGERIA - Ya zuwa yanzu dai Alhazan jihar Bauchi guda dari bakwai da sittin ne aka kaisu kasa mai tsari, domin sauke farali.
A jawabinsa ga mahajjatan, gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir Muhammed ya bukaci mahajjatan da suyi addu’a wa kasa don samun zaman lafiya, ganin cewar an tunkari yanayin zabe.
Anata jawabin babbar mai sharia’a ta jihar Hajya Rabi Talatu Umar, ta gargadi maniyyatan da su kasance masu bin doka, su kuma kaurace ma tafiya da abubuwan da kasar ta Saudi Arabiya ta hana shiga dasu kasarta.
Shima a nasa jawabin, Amirul Hajj na jihar Bauchi Sarkin Katagun Alhaji Umar Faruk ya bukaci mutanen da aka dauka domin yin hidima wa Alhazai da su tabbatar basu bada kunya ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Abdulwahab Muhammad: