Jam’iyyar PDP din ta bayyana hakan ne biyo bayan da gwamnan jihar Bala Abdulkadir Muhammed, ya sha kaye a zaben fitar da gwani na takarar kujerar shugaban kasan Najeriya da aka gudanar a makon da ya gabata a Abuja.
Idan za’a iya tunawa dai a karshen makon daya gabata ne Jam’iyar PDP, mai mulki a jihar Bauchi ta gudanar da zaben fidda gwani don yin takarar kujerar gwamnan jihar, inda aka zabi, tsohon sakataren gwamnatin jihar, Barrister Kashim Ibrahim, a matsayin wanda zai yi takara.
Amma kuma sai ga shi kasa da sati guda da gudanar da zaben fitar da gwanin, wanda aka zaba Barrister Ibrahim Kashim, ya ce ya ajiye wannan takara don kashin kansa, kuma gwamna mai-ci, Sanata Bala Abdulkadir Muhammada, shi ne zai yi takarar kamar yadda kakakin jam’iyar PDP din a Jihar Bauchi ya shaida mana.
A gefe guda kuma masu nazarin harkar siyasa, sun ce ba sa mamakin faruwar hakan, a cewar wata ‘yar siyasa Hajiya Ladi da ta shaida mana ta wayar tarho.
A halin da ake ciki kuma, ‘ya’yan babban Jojin Najeriya, Ibrahim Tanko Muhammad, su biyu sun samu nasara a zaben fitar da gwani, a shiyyar Bauchi ta Arewa, inda guda ya samu nasarar zaben fitar da gwanin a matsayin dan majalisar wakilai a jam’iyar PDP, a yayin da dayan kuma ya samu nasara don yin takarar kujerar Sanata, a Jam’iyyar APC.
Kakakin jam’iyar PDP, a jihar Bauchi ya tabbatar mana da nasarar da dan jam’iyar tasu ya samu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Abdulwahab: