An kaddamar da wannan shiri ne da ake kira BASHCMA a takaice a karamar hukumar Kirfi a matakin farko na aiwatar da shirin da za’a gudanar a dukan yankunan kananan hukumomi ashirin dake jihar
Shirin wanda aka kasa gida uku ya hada da bangaren da ya shafi kula da ma’aikata, da na wadanda basa aikin gwamnati, sai kuma na marasa galihu.
A hirar shi da Muryar Amurka, Shugaban hukumar a jihar Bauchi Dokta Mansur Dada, ya bayyana cewa, an kaddamar da ashirin ne ganin yadda duk da yake ana da kwararrun ma'aikatan jinya, da isassun magunguna da kuma asibitai, mutane da dama suna fuskantar matsalar kula da lafiyasu, sabili da rashin kudin biyan aikin jinya.
Bisa ga cewarshi, hukumar zata bada karfi wajen cike gibin da ake samu wajen kula da lafiya musamman abinda ya shafi talakawa masu karamin karfi wadanda da dama su ke mutuwa da cututukan da za su iya warkewa da sun sami jinya.
A jawabinsa, shugaban karamar hukumar Kirfi, Alhaji Garba Musa Bara, ya bayyana bada goyon bayan karamar hukumar don cimma burin Shirin.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Mohammed cikin sauti: