Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kama Mutanen Da Ake Zargi Da Kwakule Idanun Wani Yaro A Jihar Bauchi


Rundunar yan sanda
Rundunar yan sanda

Yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka, matashin da aka kwakulewa idanun ya nemi da a bi masa kadınsa.

A tattaunawa da kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Umar Sanda ya ce bayan wasu bayanai da yaron da aka kwakule masa idanu da karfin tsiya ya ba su ne, ya kai ga kama mutumin na farko mai suna Issac Ezekel, mai shekaru 32.

Ya ce “mun yi nasara kama mutum na farko wanda ta kansa ne muka kamo saura mutum biyu. Yayin da muka gabatar da Ezekel a gaban yaro da aka yi masa lahanin, daga jin muryarsa sai ya ce mana lallai mutumin da ya kwakule masa idanu kenan. Da farko ya so yana gardama amma kuma ya amince da shi ne ya yi wannan aika-aika.”

CP Umar Sanda ya ce rundunar ‘yan sanda tana nan tana gudanar da bincike a kan mutanen, yayin da aka kai yaron asibiti domin kula da lafiyarsa.

Daga bisani Issac Ezekel ya shaidawa ‘yan sanda sauran mutane biyu da suka hada da Nekson Bawa mai shekaru 38, dan garin Kabwir a jihar Filato, da kuma Yohana Luka dan garin Amper a jihar Filato dukkan mutanen suna hannun ‘yan sanda ana ci gaba da gudanar da bincike.

A ziyarar da wakilin Sashen Hausa ya kai a asibitin koyarwa na Tafawa Balewa dake Bauchi, ya ji ta bakin yaron da aka cire masa idanu, mai suna Zubairu Salisu, inda ya ce yana so a aiwatar da irin abin da mutumin ya yi masa a maimakon cewa za a bi dogon shari’a.

Mallam Salisu Katsina shine mahaifin yaron da aka kwakule masa idanu, shima dai ya bukaci ganin an bi kadin yaran nasa kamar yanda ya bukata.

Ga dai rahoton Abdulwahab Mohammed daga Bauchi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG