A yayin da tawagar motocin jakadiyar ke wucewa ta wani kauye sai matashin yayi yunkurin tsallaka hanya, daya daga cikin motocin da ke wannan tawaga ta kade shi kuma nan take ya Allah ya dauki ransa.
Sai dai Musa Usaini, wanda yake mai rajin kare yancin bil Adama a Kamaru, yayi kira ga Majalisar Dinkin Duniya, da ta fara da taimakawa yara da wadanda aka kashe da kayayyakin da suke bukata kafin a yi maganin Boko Haram din. Har ma yace dole sai an biya iyayen wannan yaro diyyar dansu.
Shima Alhaji Sani Canga, mai sanya idanu kan sha’anin gudanar da mulkin kasar jamhuriyar Kamaru, yayi kira ne da gwamnati da ta mayar da hankali wajen duba faruwar irin wannan hatsari ta kuma dauki matakin da ya dace.
Your browser doesn’t support HTML5