Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Majalisun Jihohin Kano da Bauchi Sun Dukufa Wajen Aikin Farfado Da Tattalin Arziki


Taron Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya a Kano
Taron Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya a Kano

Majalisun dokokin jihohin Kano da Bauchi sun himmatu wajen zartar da wasu dokoki da zasu inganta bangarorin hakar ma’adanai da sha’anin kasuwanci a jihohin a wani yunkuri na bunkasa tattalin arzikin jiihohin biyu.

Yunkurin majalisun jihohin biyu wani matakine na da ya dace da manufar gwamnatin Tarayya ta rage dogaro da albarkatun Mai, Hon Abdulmuminu Bala Fanti, dake zama mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi, yace tuni majalisar ta samar da wasu dokoki da zasu baiwa gwamnatin jihar damar baiwa wasu kamfanonin hada hadar ma’adanan karkashin kasa a jihar.

Inda yace Allah ya albarkaci jihar Bauchi da ma’adanai wanda kasashen duniya ma ke zuwa domin su tona, hakan yasa suka yanke shawarar da gwamnatin jiha ta kafa kamfanonin da zasu rika sayan ma’adanai daga mutanen jiha da suka tona, ita kuma gwamnatin jiha ta rika sayarwa mutanen kasashen waje.

Jihar Kano kuma majalisar dokokin jihar ce ta himmatu wajen yin garambawul ga dokokin da yarjejeniyar cinikayya tsakanin yan kasuwar jihar da na ketare musammam ma wadanda ke kwarar kasuwar jihar daga kasar China. Hon Kabiru Alasan, shine shugaban majalisar.

Wanda yace abubuwan da suke faruwa game da maganar ‘yan kasuwar kasar China, da suka baibaye harkokin kasuwanci a jihar Kano, hakan yasa sukayi kuduri da zai duba da gyara doka ta kasa da kasa da yarjejeniyar cinikayya tsakanin Najeriya da kasar China.

Baya ga gudanar da garambawul a dokokin da suka kafa hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Kano, gabanin afkuwar tsautsayin gobarar kasuwar Sabon Gari, gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, yace gwamnatinsa ta kudiri aniyar zamanantar da kasuwannin jihar, domin habaka hada hadar kasuwanci a kasuwannin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG