Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya sun bace sakamakon harin da Boko Haram ta kai kansu a Kareto


Hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai
Hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai

Da safen jiya ne wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka yiwa rundunar sojin Najeriya kwantan bauna a garin Kareto dake arewacin Borno

Harin ya zo ne bayan kwana guda da rundunar ta samu kwato makamai masu dimbin yawan gaske daga kungiyar ta Boko Haram a wasu kauyuka na jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Yanzu daruruwan sojojin Najeriya sun bace yayinda wasu suka samu tasllakawa zuwa cikin birnin Maiduguri.

Saidai bayanai dake fitowa daga yankin na nuni da cewa sojojin sun samu nasarar hallaka 'ya'yan kungiyar da dama kana su ma 'yan Boko Haram din sun raunata wasu sojojin.

Wani soja da ya sami tsallakawa daga Kareto zuwa Maiduguri ya shaidawa Muryar Amurka cewa sun yi kwana biyar suna jiran za'a kawo masu makamai ba'a kawo ba sai sabbin sojoji. Yace da safe da misalin karfe biyar mutanen suka farmasu da manya manyan makamai. Sun kashe wani dan kunar bakin wake. Yace motarsu ta mutu bata tafiya haka suka far masu amma sun kashe wasunsu da dama.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG