A cikin kasafin ne take harsashen abun da zata samu da kuma zata kashe da abubuwan da zata kashe kudaden a kai.
Kasafin kudi nada mahimmanci saboda duk wanda yake son ya yi muamala da gwamnati zai so ya ga inda ta mayarda hankalinta. Menene take son ta yi yaya kuma zata yi su. Kasafin kudi na bada hanya dalla dalla ta yadda za'a samo kudi da yadda za'a sarafasu.
Hanyoyin sarafa kudaden zasu nuna ko tattalin arziki zai habaka ko ba zai habaka ba.
Kudin da ake tsarawa ba a ajiye yake ba harsashe ne. Babu mamaki idan gwamnati tana da rarar kudi tana iya hada abun da take sarafawa dasu. Amma mafi yawa zata ayyana matakan da zata bi bisa ga abun da take tsammani zata samu.
Babban bangaren dake kawowa gwamnati kudi shi ne haraji. Saboda haka yakamata a gani wane irin haraji gwamnati zata sa wannan shekarar. Daga cikin kasafin kudi ake gane wace alkibla ta sa gaba.
Wata hanya kuma da za'a lura ita ce yadda gwamnati zata kashe kudin. Idan za'a kashesu akan ayyukan yau da kullum mutane zasu samu aiki rayuwar jama'a kuma zata canza. Kowa zai ci albarkacin kudin dake zagayawa a cikin kasa.
Idan ba'a tabbatar da kasafin kudi ba manyan ayyuka basa yiwuwa, ayyukan da zasu shafi rayuwar al'umma .
Ga karin bayani.