A karshen watan gobe ne gwamnatin zata cika shekara daya akan karagar mulkin kasar ta Najeriya.
Cikin lokacin karancin man fetur da rashin wutar lantarki da zafin talauci sun addabi al'ummar kasar lamarin da wasu suke gani watakila ba za'a samu fita ba.
'Yar majalisar jihar Neja Binta Mamman ta kira mutanen Najeriya a kara hakuri da yanayin da kasar ke ciki. Tace dama duk abun da dan Adam yake nema baya samunsa cikin sauki.Da yaddar Ubangiji da hadin kan 'yan kasar za'a cimma nasara.
Isa Tafida Mafindi tsohon dan PDP da ya jingine jam'iyyar bayan babban zaben da ya kawo Buhari kan mulki yace suna gayawa 'yan Najeriya kowa ya yi hakuri domin ba'a yi zaben tumun dare ba..Gwamnatin yanzu ta shimfida turbar sarafa Najeriya yadda kowa zai samu walwala.
A nasa bangaren dan kasuwa Ado Adamu yana ganin sai shugaban ya yi takatsantsan kan yarjejeniya musamman da kasar China ko Sin. Daga yanzu yace shugaban kasa ya daina tafiya ya nada kwamiti ya je domin lokaci na kurewa. Yanzu yana da shekaru biyu da rabi ne kawai na mulki.
Malamai irinsu Shaikh Bala Lau na kiran a dinga yiwa shugaban addu'a.
Ga karin bayani.