Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin kare hakkin jama'a na adawa da gyara dokar kotun da'ar ma'aikata


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

A daidai lokacin da shugaban majalisar dattawan Najeriya ke fuskantar shari'a a kotun da'ar ma'aikata sai gashi majalisar dattawan tana yunkurin yiwa dokar kotun gyaran fuska lamarin da ya harzuka kungiyoyin kare hakkin jama'a ishirin da takwas

Gyaran da majalisar take son ta yi yana neman a cire kotun ne daga karkashin ikon sakataren gwamnati zuwa karkashin ma'aikatar shari'a.

Haka kuma gyaran na bukatar kotun ta zama wadda zata kaucewa siyasa.

Wannan matakin gyara dokar da ta kafa kotun ya dauki hankalin kungiyoyin kare hakkin jama'a ishirin da takwas har ma sun kira taron manema labarai a Abuja domin bayyana adawarsu da yukurin.

Eze Nwago shugaban kungiyar dake kare ka'idojin zabe yace menen ake gyarawa kuma don me ya sa za'a gyara yanzu. Me ya sa basu gyara da ba. Yace gyaran basa bukatansa yanzu musamman lokacin da shugaban majalisar ke gaban kotun yana fuskantar tuhuma.

Shi ma Kola Banwo shugaan wata kungiya ya yi tsokaci. Yace sabili da mutum daya da yanzu dokar ta shafa sai a yi yunkurin yiwa dokar kwaskwarima.Idan ana yawan canza dokoki ba gaira ba dalili to mulkin dimokradiya ya kare ke nan. Sai a gyara doka saboda mutum daya a kasar da take da mutane miliyan dari da saba'in bai dace ba.

Masu sharhi a alamuran yau da kullum su ma sun tofa albarkacin bakinsu. Mustapha Marafan Gayya yace bai kamata su bari irn wadannan rigingimun na faruwa ba. Misali ana cewa Bukola Saraki shugaban majalisar da Bola Tinubu uban jam'iyyar APC basa shiri. Ya kira 'yan APC su natsu su yi hadin kai.

Shi kuwa Bashir Baba ya yi mamakin yadda majalisar ta yi saurin kawo gyaran. Yace ko kunya bata ji ba. Bata tashi yin gyaran ba sai lokacin da Bukola Saraki shugabanta ya tsinci kansa a wani halin tafka rashin gaskiya kana ta san zata yi gyara. Wannan ya nuna 'yan majalisar dattawan ba jama'a suka zo su yiwa aiki ba suna yiwa kansu ne.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG