Kimanin 'yan gudun hijira dari takwas daga rikicin Boko Haram ne gwamnatin jihar Neja ta budewa sansanoni guda uku cikin jihar.
Gwamnatin jihar tace ta yi tanadi na musamman wa 'yan gudun hijiran domin kyautata masu. Yanzu an yi masu sansanoni a kananan hukumomi uku.
Alhaji Ibrahim Inga shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar yace gwamnan jihar ya basu kudi sun yiwa 'yan gudun hijirar jiragen ruwa domin yawancinsu masunta ne. Gobe ne zasu raba masu. Haka ma masu bukatar mashin da suke sana'o'i daban daban su ma an saya masu.
Gwamnatin ta yi masu tanadin kayan abinci. Duk kayan gobe za'a raba masu. Gwamnan ya bada kudi sama da miliyan goma sha biyar da suka sayi kayan dasu.
A halin da ake ciki hukumar bada agajin gaggawar ta kai kayan tallafi wa wadanda isakar damina ta kwarewa gidaje a garin Kagara. Akwai wadanda gidajensu sun kware babu inda zasu kwana. Akwai kudi da aka basu da kayan sake gina gidajensu.
Wasu da suka samu tallafin sun yi bayani. Magajin askar Kagara yace gidansa dakuna goma sha daya ne kuma ya rushe. Gwamnati ta taimaka masa da nera dubu hamsin da kwanun jinka amma yana korafin kudin bai isa ba.
Ga karin bayani.