Zasu Marawa Shugaba Buhari Baya Dari Bisa Dari

Fiye da watani biyu kennan da kaddamar da majalisun dokokin Najeriya da aka yi amma zaman da suka yi bai wuce na makoni ukku, ba, wannan ya sanya su yiwa kansu fada wajen mahawara akan wasu batutuwa da suka shafi kasa irin na faduwar darajan Naira, da batun kai dauki gas ashen Arewa maso gabashin Najeriya.

Sanata Dino Malaye, ya bayyana abubuwan da suka fi baiwa mahimmanci, yana cewa “yanzu babu wani matsala a Majalisa, shi shugaban majalisa Dattijai, ya kama aikin dake gaban shi, mu yanzu talakawan Najeriya, su suka damemu kuma mun riga mun sa maganar su a gaba kuma an fara dauka matakai da zasu tattara arzikin kasa.”

Ya kara da cewa zasu marawa shugaba Muhammadu Buhari, baya dari bisa dari da kuma tamakawa kan gyaran da yake so yayi a Najeriya, da kuma batun kwato kudaden da aka yi sama da fadi dasu.

Sai dai rashin nada shugabanin kwamitocin majalisar wadanda sun eke zaburar da aikin ‘yan majalisa ya kasance abun dake rage azamar aikinsu.

Koda yake ana kallon majalisar a matsayin wace ta samu natsuwa dama zaman lafiya a cikin ta masamman ganin yadda a farko an yamutsa gashin baki da kuma tada jijiyar wuya dama baiwa hammata iska.

Gaskiya ko akasin haka zata bayyana a lokaci da shugaba Buhari zai aika da jerin sunayen mutanen da yake so a nada su ministoci, za’a gani ko ‘yan majalisar zasu yi tutsu irin na Jaki ne koko a’a.